Sakataran harkokin wajen Amirka Antony Blinken na ziyara a Turkiyya | Labarai | DW | 20.02.2023
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakataran harkokin wajen Amirka Antony Blinken na ziyara a Turkiyya

Sakataran harkokin wajen Amirka Antony Blinken ya fara ziyarar aiki a Turkiyya kwanaki 14 bayan girgizar kasa da ta auku a kasar da makwabciyarta Siriya.

Wannan ziyarar ta babban jami'in diplomasiyar na Amurka na zuwa ne bayan sanarwa da Amurkan ta yi na ba da tallafi na dala miliyan guda na kudin kasar Amurka ga Turkiyya.

Antony Blinken zai gana a wannan Litinin da shugaban kasar Turkiyya  Recep Tayyip Erdogan a ziyarar nuna alhinin wacce ke zuwa kwanaki 14 bayan munmunar girgizar kasar da Turkiyya da Siriya suka fuskanta tare kuma da tattauna batun cinikin jiragen yaki da Tukiyya ke son saya daga Amirka.

Zai a yi ganawar ne bayan ziyarar guraren da suka fuskanci wannan ibtila'i inda ma'aikatan ceto da na agaji sama da 265.000 na kasar Turkiyya da kuma karin wasu 11.500 daga kasashen Duniya suka bazama domin lalubo gawarwakin mutane daga baragujen gine-gine. 

Ko baya ga batun ibtila'in mafi mufi muni da Turkiyyar ta fuskanta, ana sa ran za su tattana kan batun yakin Ukraine da Rasha da kuma kin sahalewa kasashen Sweden da Finlande kokarinsu na shiga kungiyar kawancen tsaro ta NATO da Turkiyyar ta yi.