Sakamakon zaben ′yan majalisu a Burundi | Labarai | DW | 02.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakamakon zaben 'yan majalisu a Burundi

Al'ummar kasar Burundi na can na dakon sakamakon zabukan majalisar dokoki da suka gudanar a Litinin din da ta gabata.

Zaben 'yan majalisun dokoki a Burundi

Zaben 'yan majalisun dokoki a Burundi

Jam'iyyun adawar kasar dai sun kauracewa zabukan domin ci gaba da nuna adawarsu da yunkurin shugaban kasar Pierre Nkurunziza na yin tazarce a karo na uku a kan shugabancin kasar. Rahotanni sun tabbatar da cewa sama da mutane 70 ne suka rasa rayukansu tun bayan barkewar gagarumar zanga-zangar adawa da shirin tazarce na Shugaba Nkurunziza a kasar.