Sace ma′aikacin gwamnati a Kamaru | Labarai | DW | 26.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sace ma'aikacin gwamnati a Kamaru

Wasu mutane dauke da makammai sun sace wani babban jami'in gwamnati a garin Batibo da ke yankin da ake magana da turancin Ingilishi a Arewa maso yammacin kasar Kamaru.

Hukumomin gundumar ta Batibo sun tabbatar da wannan labarin inda suka ce an taras da motar ma'aikacin gwamnatin da aka sace akone kurmus. Tuni dai 'yan kungiyar ADF ta Amazoniya Defense Forces da ke yankin da ake magana da turancin Ingilishi wadda Lucas Cho Ayaba ke jagoranta ta dauki alhakin sace ma'aikacin kamar yadda ta wallafa ta shafukan sada zumunta. Dam dai a ranar 11 ga watan na Febrairu ne aka sace shugaban gundumar ta Batibo wanda har yanzu ba'a kai ga gano inda yake ba. Lamarin Arewa maso yammacin kasar ta Kamaru dai ya kara tabarbarewa, tun bayan kame mayan 'yan awaran guda 47 tare da babban jagoransu Sisiku Ayuk Tabe a Najeriya, tar kuma da mika su ga hannun hukumomin ta Kamaru.