Sabuwar jam′iyya ta yi tasiri a Faransa | Siyasa | DW | 12.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sabuwar jam'iyya ta yi tasiri a Faransa

Sakamakon zaben majalisar dokoki da ya gudana a kasar Faransa, ya nunar cewa sabuwar jam'iyyar sabon Shugaban kasar Emmanuel Macron da jam'iyyar da ke kawance da ita ta Modem, sun sami rinjaye a majalisar dokoki.

Kama daga kafofin yada labarai, zuwa ga sauran 'yan siyasa da dama ne suka bayyana ra'ayoyi mabambanta bayan samun sakamakon zagayen farko na zaben 'yan majalisar dokokin kasar ta Faransa, wanda ya kai jam'iyyar La République en marche ta Shugaba Emmanuel Macron tare da abokiyar kawancenta Modem, suka yi wa sauran jam'iyyun kasar fintinkau. Alkaluman farko dai sun yi nunin cewa sun sami galaba ne da kashi 32.32 cikin 100 na kuri'un da aka kada.

Sai dai kuma masharhanta sun dubi batun rashin fitowar jama'a domin kada kur'ia a matsayin wani babban kalubale. Amma da yake magana jim kadan bayan sakamako na farko na zaben, Firaministan kasar Faransa Edouard Philippe ya nuna farin cikinsa, inda ya ce Faransawa sun isar da babban sako.

"Duk da karancin masu zaben, sakon da Faransawa suka aike ba shi da wata tantama. A karo na uku a jere, kun sake nuna goyon bayanku ga tsarin kawo sauyi na Shugaban kasa, kuma a ranar Lahadi mai zuwa, majalisar dokoki za ta dauki sabuwar fuska a Faransa."

Da wannan sakamako na kashi 32.32 cikin dari da ta samu a wannan zabe, ana hasashen sabuwar jam'iyyar tare da abokiyarta ta Modem, za su samu kujeru daga 400 zuwa 455 cikin kujeru 577 da ake da su a kasar baki daya; wanda ake ganin za kawar da duk wata bukata ta yin kawance da jam'iyyar 'yan Republicain mai kawance da UDI da suka samu kashi 21.5 cikin 100 na yawan kuri'un, da suke fatan kullawa da sabon shugaba Macron. Kuma 'yan kasar ta Faransa da dama na ganin samun babban rinjaye shi ne zai bai wa shugaban damar shinfida tsarinsa na kawo sauye-sauye a kasar.

Su kuwa masu goyon bayan jam'iyyar 'yan gurguzu ta tsohon shugaban kasa Francois Hollande, jam'iyyar da ta yi mummunar faduwa a kasa warwas da kashi 09.5 cikin 100, sun bayyana yadda zaben ya firgitasu suka yi. Sakamakon zaben dai ya nunar cewa, jam'iyyar Front National ta Marine Le Pen mai akidar kyamar baki, ta zo ta uku ne da kashi 13.2 cikin 100 wanda ake ganin hakan ka iya ba ta kujeru hudu a majalisar.

Zaben na Faransa dai batu ne da aka bibiye shi sau da kafa a kasashen Turai, musamman ma manyan makwabtanta irinsu Jamus, inda kama daga jaridunsu da ma wasu 'yan kasar suka yi tsokaci kan zaben Egbert Lux wani dan kasar ta Jamus ne.

"Haka, na ji dadin yadda jam'iyyar shugaba Macron ta yi kokari. Ina tsammani wannan babbar dama ce ga Tarayyar Turai musamman, ganin cewa masu goyoyn bayan Turai ne suka nasara. Lallai wannan ya yi armashi."

Shi ma dai wani dan kasar ta Jamus mai suna Christopher Stock shi kuma fata ya yi na ganin su ma sun sami wani mai kamar sabon shugaban na Faransa da ke da kyaukyawar niyya ta ciyar da kasarsa da ma tarayyar Turai gaba.

"Ina fata mu samu wani kamar shi. Ba 'yan siyasa da za su dauki matakin da babu wani buri, sai sun duba ra'ayin mutane kafin su yi gyara. Komai zai sauya ina tsammani."

Jam'iyyar La Farance Insoumise ta Jean Luck Melenchon da ta shi da kashi 11 cikin 100 za ta iya samun kujeru daga 10 zuwa 23 a majalisa. Sai dai adadin wadanda ba su yi zaben ba ya kai kashi 51.29 cikin 100, inda 'yan siyasan za su yi kokarin bai wa masu zaben kuzari a zagaye na biyu da zai gudana ranar Lahadi 18 ga wannan wata na Yuni.