Sabon yunkurin ceto ilimin boko a Najeriya | Zamantakewa | DW | 30.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Sabon yunkurin ceto ilimin boko a Najeriya

Matakin da shugaban Najeriya ya dauka ta hanyar dauka da horas da malaman makaranta dubu 500 a 2016 zai yi tasiri a kokarin ceto ilimin boko da ke fuskantar mummunar koma baya.

Tun shekarar 1976 da gwamnatin Najeriyar ta ayyana samar da ilimi kyauta ba tare da tanajin da ya dace ba ne dai aka fara fuskantar koma baya a harkar ilimin firamaren kasar. Wannan matsalar ta ci gaba da jefa matsayin ilimin cikin mummunan hali duk da matakai na kokarin ceto wannan sashi. Samar da tanaji a kasafin kudin 2016 da shugaba Muhammadu Buhari ya yi na daukan malamai rabin miliyan don horar da su a tura su makarantun firamare na zama sabon yunkuri.

Shin wadanne matakai ya kamata a dauka ne? Mallam Ahmad Tijjani kwararren malami ne kuma sakataren gudanarwa na kungiyar tsaffin daliba na makarantun gwamnatin tarayyar Najeriyan ya ce akwai matakan da ya kamata a yi la'akari da su domin samun nasara.

"A samu malami kwararre wanda kuma za a biya shi yadda ya kamata. Sai kayan aiki su suka fi muhimmanci da kuma aji. Za a dauki tsawon lokaci kafin wannan ya yi tasiri."

Laifin tabarbarewar ilimi ya shafi kowa

Halin da ilimin Najeriya ya shiga ya sanya ganin tururuwar da daliban kasar ke yi zuwa kasashen da ba su ma kai matsayin Najeriyar ba. To sai ga Danladin Shehun Biba sakataren ilimi a yankin Suleja a jihar Neja, na mai bayyana kwarin guiwa a kan kwarewar malaman Najeriyar, sai dai kawai rashin samun halin da za su nuna kwarewar ta su.

"Alal hakika iliminmu bai tabarbare irin yadda ake tsammani ba. Ko wane bangare na da laifi wurin tabarbarewar ilimin. Gwamnati na da laifi, iyaye na da laifi, sannan malamai ma suna da irin na su laifin. Gwamnati ba ta daukan nauyin malaman yadda ya kamata ta ba su ainihin abin da zai karfafa musu guiwa. Shi ya sa sai ka ga makami kwararre ya gudu ya kama siyasa ko ya gudu ya koma aikin banki idan yana da ilimin aikin banki."

To ko wane tasiri wannan yunkuri zai yi ne sanin cewa an dade ana kokarin ceto ilimin boko a matakin firamare a Najeriyar? Har ila yau ga Mallam Ahmad Tijjani.

"Alal hakika duk wanda ya yi digiri ka dauke shi ka ba shi horo mai kyau zai yi aiki fiye da yadda ake zato. Sannan kuma a rage yawan cunkoson yara a cikin aji."

Kokarin maido da martaba da ma matsayin ilimin Najeriya zai taimaka wa 'ya'yan marasa karfi samun ilimi mai daraja, da ma kyautata matsayin ilimin boko da ka iya rage tururuwar al'ummar kasar zuwa kasashen da ba su kai matsayin Najeriyar ba domin neman ilimi.