Sabon tashin hankali a Turkiya
August 28, 2014Talla
Rahotanni daga ƙasar Turkiya na nuni da cewar jami'an 'yan sandan ƙasar sun yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar nuna adawa da sabuwar gwamnatin ƙasar. Zanga-zangar dai da cibiyoyin al'umma na ƙasar suka shirya, sun shiryata ne domin nuna adawa da sabon shugaban ƙasar Recep Tayyip Erdogan da aka rantsar da sanyin safiyar Alhamis ɗin nan. Wannan dai shi ne karon farko a cikin watanni uku da suka gabata a ƙasar aka samu wani sabon tashin hankali.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Abdourahamane Hasane