Sabon sharadi kafin Girka ta samu bashi | Labarai | DW | 12.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon sharadi kafin Girka ta samu bashi

Rukunin kasashen da ke amfani da Euro ya sake gindawa Girka sharadin albarkantar dokar sauye-sauyen tattalin arziki kafin ya tattana batun bashin da ya yi mata katutu

Ministocin kudi na kasashen da ke amfani da takadar kudin Euro sun dibarwa Girka wa'adin Laraba mai zuwa, don ta nuna cewar da gaske take yi za ta aiwatar da matakan tsuke bakin aljuhu da ta bayyana, kafin su bude sabon babin tattaunawa da ita a kan bashin da take bukata. Cikin wata takardar hadin guywa da suka mikawa shugabannin kasashen naTurai wadanda suka yi taro a Bruxelles, ministocin sun bukaci majalisar Girka ta albarkanci kudiri doka da ta shafi sauye-sauyen tattalin arziki kan nan da kwanaki uku masu zuwa.

Kasashen 19 da ke amfani da takardar kudin Euro suna ci gaba da samun rarrabuwar kawuna kan matakan da ya kama a dauka a kan kasar Girka, dangane da rikicin kudi da ya zo mata iya wuya. Faransa na kai goro da mari don ganin cewar an ci gaba da damawa da Girka a cikin rukunin kasashen da ke amfani da Euro, yayin da Jamus take nuna dari-dari kan sake rantawa Girka wasu makudan kudade ba tare da samun tabbacin cewar za ta iya biyan wannan gammon bashin da ya yi mata katutu ba.