Sabon rikici ya sake barkewa a Masar | Labarai | DW | 26.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon rikici ya sake barkewa a Masar

Hukumomi a kasar Masar sun ce kimanin mutane goma sha shidda sun kwanta dama a yankin Port Said biyo bayan boren da al'umma su ka yi a wannan Asabar din.

Egyptians demonstrators scatter during clashes with riot police in Tahrir Square on January 25, 2013. Huge crowds are expected to demonstrate in Egypt on the second anniversary of the revolution that ousted Hosni Mubarak and brought in an Islamist government, as political tensions simmer and economic woes bite. AFP PHOTO/MOHAMMED ABED (Photo credit should read MOHAMMED ABED/AFP/Getty Images)

Ägypten Kairo Demonstrationen am zweiten Jahrestag der Revolution 25. Januar 2013

Tashin rikicin ya samo asali banyan da wata kotun kasar ta Masar ta yankewa wasu mutane ashirin da daya hukuncin kisan kai sakamakon samun su da hannu da kotun ta ce ta yi a hatsaniyar da aka yi a wani filin wasan kwallon kafar kasar wanda ya yi sanadiyyar rasuwar mutane da dama a bara.

Daga cikin wadanda su ka rasu a hargitsin na yau dai har da jami'an 'yan sanda guda biyu yayin da hukumomin asibitin da ke yankin na Port Said su ka ce kimanin mutane dari biyu sun jikkata.

Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan da aka samu tashin hankali a a sassa daban na kasar ta Masar daidai lokacin da ake bikin tunawa da juyin-juya halin da ya kawar da shugaba Hosni Mubarak daga gadon mulki, bikin da ya rikide ya zama tashin hankali wanda ya sanya mutane takwas su ka rasu yayin da wasu dama su ka jikkata.

Tuni dai hukumomi a yankunan da rikicin ya shafa su ka jibge jami'an tsaro don yin sunturi saboda gudu sake barkewar rigima.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Saleh Umar Saleh