Sabon rikici na barazanar barkewa a Sri Lanka | Labarai | DW | 25.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon rikici na barazanar barkewa a Sri Lanka

Wasu ´yan bindiga da ba´a gane su ba sun harbe dan majalisar dokoki na kabilar Tamil Joseph Pararajasinham har lahira a lokacin da yake halartar addu´o´in bukin Kirismeti a wani coci dake gabashin kasar Sri Lanka. Hakan dai ya zo ne bayan wani harin kwantan bauna a ranar juma´a wanda yayi sanadiyar mutuwar sojojin ruwa 13. Gwamnati ta zargi ´yan tawayen Tamil Tigers da kai harin, ko da yake kungiyar ta musanta haka. A kuma halin da ake ciki wakilan kasashen Asiya da na Turai sun gana da shugaban siyasar Tamil Tigers a wani yunkuri na hana barkewar wani sabon rikici. Shugaban Tamil S.P. Thamilselvan ya tabbatarwa wakilan daga Japan, Norway, Amirka da kuma KTT cewa ´yan tawayen na biyayya ga shirin samar da zaman lafiya. A shekara ta 2002 aka yi shailar tsagaita bude wuta tsakanin gwamnati da ´yan tawaye.