Sabon harin ta′addanci a Najeriya | Labarai | DW | 21.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon harin ta'addanci a Najeriya

A kalla mutane 45 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da wasu da ba a san ko su wanene ba suka kai a kauyen Azaya Kura cikin jihar Borno, jihar da ke fama da rikicin Boko Haram

Shaidun gani da ido dai sun ce akwai yiwuwar adadin wadanda suka hallaka ya fi haka kasancewar su a yanzu sun tsere ne zuwa kauyukan da ke makwabtaka da su. Maharan dai sun zo ne cikin manyan motocin daukar kaya cike da makamai, inda suka farwa al'ummar kauyen na Azaya Kura. Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan hari, sai dai kungiyar Boko Haram da ke gwagwarmaya da makamai a kasar, ta saba kai irin wadannan hare-hare. Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da shugaban Najeriyar Goodluck Jonathan ke neman majalisar dokokin kasar ta amince masa ya kara wa'adin dokar ta-baci jihohi uku dake yankin arewa maso gabashin kasar a karon na hudu. Batun da majalisar dokokin kasar ta samu rarrabuwar kauna a kansa inda akarin basa goyon bayan bukatar ta kara tsawaita wa'adin dokar ta-bacin. A jiya Alhamis dai, yan majalisar dokokin da ma'aikatansu suka sha hayaki mai sa hawaye daga jami'an 'yan sanda, a yayin da wakilan majalisar dokokin ke kokarin shiga domin tattauna batun tsawaita dokar ta-bacin.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Usman Shehu Usman