Sabon harin bam a Potiskum | Labarai | DW | 24.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon harin bam a Potiskum

Akwai fargabar mutane 17 sun riga mu gidan gaskiya wasu 27 kuma sun jikata bayan wani da ake zaton dan kunar bakin wake ne, ya tada Bam.

Wannan lamari ya afku ne a wata tashar mota da ake kira tashar dan Borno a garin Potiskum a jihar Yobe. Shaidun gani da ido sun bayyana cewa mutumin ya shiga tashar ne inda ya nemi motar dake lodi ya biya ya shiga sannan ya tashi Bam din tare da hallaka mutane da dama. Wani da ya kasance ganau ya shaidawa DW abinda ya faru ta wayar tarho.

Ya zuwa yanzu babu cikakkun alkaluma na yawan wadan da suka mutu sanadiyyar wannan hari inda kuma hukumomi ko jami'an tsaro ba su kai ga cewa komai akai ba. Wannan dai shine karo na biyu da ake samun fashewa a garin Potikum wanda ke zama mafi samun irin wadan nan hare tsakanin biranen shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya.