Sabon harin ƙunar baƙin wake ya halaka mutane 8 a Afghanistan | Labarai | DW | 20.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon harin ƙunar baƙin wake ya halaka mutane 8 a Afghanistan

Akalla mutane 8 sun rasu sannan wasu 35 sun samu raunuka a wani harin kunar bakin wake da aka kai a lardin Paktia dake kudancin Afghanistan. Harin bayan bayan nan ya auku ne a garin Gardez lokacin da wani dan kunar bakin wake ya ta da bam a kusa da wani ayarin dakarun kasa da kasa a kusa da wata kasuwa. Wannan harin ya zo ne kwana guda bayan wani harin kunar bakin wake da aka kai jiya asabar a birnin Kunduz wanda ya halaka mutane 9 ciki har da sojojin Jamus su 3. ´Yan tawayen taliban sun yi ikirarin kai wannan hari, wanda shi ne mafi muni da aka taba kaiwa akan sojojin Jamus a Afghanistan cikin shekaru 4 da suka gabata. A kuma halin da ake ciki ministan tsaron Jamus Franz-Josef Jung ya ce dakarun kasarsa zasu ci-gaba da aikin da suke a Afghanistan.