Sabon hari a wani Masallaci a Maiduguri | Labarai | DW | 27.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon hari a wani Masallaci a Maiduguri

Wasu mahara sun hallaka, bayan da suka kudiri aniyar kai hari a wani Masallaci a birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Nigerien Maiduguri Autobombe Doppelanschlag März 2014

Harin bam a wurin taron jama'a ba bakon abu ne ba a Borno

Shaidun gani da ido sun nunar da cewa maharan da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne, sun yi nufin shiga sahun sallah a lokacin da ake sallar "Tahajjud" cikin daren Lahadi 26 ga wannan wata na Yuni da muke ciki. Wani mamba a kungiyar 'yan kato da gora Babagana Kolo ya fada wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, ababen fashewar biyu ne suka tashi a wajen wannan Masallaci da ke kan hanyar Damboa. Babu dai wanda ya rasu cikin masallata sai dai kawai 'yan kunar bakin waken ne abin ya shafa, baya ga 'yan kato da gorar da suka hana su danganawa da Masallacin da suka sami 'yan raunika. Wannan dai na sake kara haskaka irin barazanar da mayakan Boko Haram din ke da ita cikin ayyukansu na ta'addanci a Najeriya.