Sabon babi a dangantakar Amirka da Najeriya | Siyasa | DW | 20.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sabon babi a dangantakar Amirka da Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, yanzu dai ya na da kyakkyawar dama, a ziyarar da ya fara a Washington, domin gyara yadda Amirkawan suke kallon kasarsa.

Deutschland G7 Gipfel Elmau Barack Obama und Muhammadu Buhari

Shugaba Obama da Buhari na Najeriya

Najeriya ta na da karfin da za ta iya kasancewa abokiyar hulda mafi muhimmanci ga Amirka a nahiyar Afrika, inji Peter Pham na cibiyar Atlantic Council yayin hira da tashar DW. To sai dai ya kara da cewar Wannan hange bai wuce fatan yiwuwar hakan ba, domin kuwa har yanzu buri na Najeriya na kasancewar babbar kawar Amirka mafi muhimmanci a Afirka bai tabbata ba.

Shima Richard Joseph, masani kan al'amuran Afirka a cibiyar Brookings a Washington ya ce raunin daraja da kimar Najeriya a idanun Amirka, ba zai rasa dangantaka da munanan hare-haren da 'yan tarzoma suke ci agaba da kaiwa a kasar ta Najeriya ba. A bisa hangen mafi yawan Amirkawa, kuma, Najeriya cike take da cin rashawa, kuma babu wani tsari da ke aiki a cikiinta. Babban abin da yafi mamaye kanun labarai bai wuce ci gaba da samun hare-hare na kungiyar tarzoma ta Boko Haram ba.

Nigeria Selbstmordanschlag in Zabarmari

Ragowar ta'addancin Boko Haram

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, yanzu dai ya na da kyakkyawar dama, a ziyarar da ya fara a Washington, domin gyara yadda Amirkawan suke kallon kasarsa. Saboda haka ne Peter Pham yake ganin ganawar da za a yi tsakanin shugaba Muhammadu Buhari da takwaransa na Amirka, Barack Obama a matsayin matakin farko na neman sabunta dangantaka tsakanin Amirka da Najeriya.

Boko Haram kalubale a yanki

Ya ce: Ziyarar ana iya ganinta a matsayin matakin farko na gyara dangantaka tsakanin Amirka da Najeriya, musamman sakamakon yakin kawo karshen 'yan kungiyar Boko Haram. Kungiyar ta 'yan tarzoma ta yi mubayi'a ga kungiyar IS, kuma a baya-bayan nan ne ta fadada hare-harenta zuwa Chadi da Nijar, abin da ke kara zama barazana ga tsaron yankin baki daya".

Nigeria Präsident Amtseinführung von Muhammadu Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari na rantsuwar kama aiki

Dangantaka tsakanin Najeriya da Amirka ta yi tsami matuka, karkashin mulkin tsohon shugaba Goodluck Jonathan, wanda Buhari ya gajeshi. Ana dai sa ran babban abin da zai dauki hankali a ganawar shugabannin biyu shi ne yaki kan kungiyar Boko Haram. A bisa ra'ayin shugabanni a Washington, Muhammadu Buhari ya na iya zama mutumin da ya dace da kokarin da ake yi na kawo karshen aiyukan kungiyar Boko Haram. Tun ma a makonnin farko da ya karbi mulki, tsohon Janar din ya nuna cewar ya na da karfin zuciyar daukar matakai masu tsanani. A 'yan kwanakin baya ya kori manyan shugabannin rundunonin sojank kasar, inda ya maye gurbinsu da wasu. Tun kafin hakan, sai da ya sanar da cewar hedikwatar rundunart saron Najeriya za ta koma zuwa Maiduguri a arewa maso gabashin kasar, domin ci gaba da yaki da Boko Haram. To sai dai ko bayan daukar wadannan matakai, hare-haren kungiyar ba su sassauta ba.

Kimar Najeriya a idanun duniya

Nigeria Poster von Präsident Mohammadu Buhari vor Militär

Dakarun tsaron Najeriya

To sai dai a cewar Richard Joseph a lokacin ziyarar da yake yi yanzu a Washington, shugaba Buhari yana bukatar samun nasarar karfafa dankon zumunci tsakanin kasarsa da Amirka. Wannan ma ya na daya daga cikin abubuwan da ke kan gaba a tattaunawar da zai yi a fadar White House, musamman saboda ganin cewar a idanun Amirka da kasashen Turai, har ma da kasashe makwabta, rundunar sojan Najeriya mutuncinta ya zube, saboda ta nuna kasawarta a yaki da kungiyarta Boko Haram, inji Peter Pham.

Ya ce: "A bara an sami banbancin ra'ayi tsakanin Najeriya da Amirka har ya zuwa matsayin da aka dakatar da shirin da aka yi inda sojojin Amirka za su horas da bataliyoyin sojan Najeriya kan dabarun yaki da amfani da makamai.

Bayan al'amuran tsaro, da yaki da Boko Haram, batun ciniki da hadin kan tattalin arziki za su zama muhimmai a tattaunawar da Buhari zai yi a Washington. Ko da shike Najeriya kan takarda, ita ce kasar da ta fi karfin tattalin arziki a Afirka, kuma ita ce tafi samar da man fetur a nahiyar, to amma akwai gibi mai zurfi tsakanin karfin tattalin arzikin da ake cewar Najeriya ta na da shi da kuma yadda yake a zahiri. Bugu da kari kuma, gwamnatin Barack Obama tana ci gaba da nuna damuwa a game da matsayin kare hakkin dan Adam a kasar ta Najeriya.

Sauti da bidiyo akan labarin