Sabbin hare-hare a Najeriya | Labarai | DW | 24.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabbin hare-hare a Najeriya

Masu aikin ceto da jami'an tsaro sun tabbatar da asarar rayuka a wasu jerin hare-haren da wasu 'yan mata uku da namiji daya suka kai wasu yankuna da ke bayan garin Maiduguri.

Rahotannin da ke fitowa daga arewa maso gabashin Najeriya, na cewa wasu mutane bakwai sun mutu a wasu hare-haren kunar bakin wake da ake alakantasu da mayakan Boko Haram. Masu aikin ceto da ma jami'an tsaro sun ce harin farko ya auku ne a kauyen Mammanti mai tazarar kilomita 15 a gashin birnin Maiduguri.

A cewarsu wasu 'yan banga sun yi kokarin dakatar da wasu 'yan mata uku dake dauke da bama-bamai da asubahin yau, inda biyu daga cikinsu suka tarwatsa kansu, dayar kuwa soja ya harbe ta. An kuma sami wani dan banga daya da ya rasa ransa a harin.

Akwai ma wani dan kunar bakin waken namiji da ya shiga kauyen Mainari da ke yammacin birnin Maiduguri, ya kuma kashe 'yan banga uku tare da raunata wasu biyu.