Sabanin Jamus da wasu kasashe kan Turkiya | Labarai | DW | 07.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabanin Jamus da wasu kasashe kan Turkiya

Shugabannin kasashen Turai da dama sun nisanta kansu daga shawarar da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayar ta ganin Kungiyar EU ta dakatar da tattaunawa da Turkiya a game da batun shigarta a cikin kungiyar.

Shugabannin kasashen Turai suka ce dakatar da tattaunawar da ake yi da Turkiya a game da batun shigarta cikin kungiyar EU ba zai kasance alkhairi ga kasashen Turan su kansu ba.  Firaministan Estoniya Sven Mikser na daga cikin masu irin wannan ra'ayi:

"Dangane da batunTurkiya a matsayinta na mai neman shiga kungiyar Tarayyar Turai ba na goyon bayan Kungiyar ta EU ta yanke hukunci da garaje a wannan shekara"

A ranar Lahadin da ta gabata ce dai shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ta bayyana bukatar tattaunawa da sauran shugabannin kasashen Turai domin yin baki guda wajen daukar matakin dakatar da tattaunawa da Turkiya kan batun shigarta Kungiyar EU, Kalaman da Shugaba Recepp Tayyip Erdogan ya bayyanasu da cewa kalaman 'yan Nazi ne. 

Tun a shekara ta 2005 ne dai bangarorin biyu suka soma tattauna batun shigar kasar ta Turkiya a cikin EU, amma abin ke cin tura musamman dangane da zargin da wasu kasashen Turai ke yi wa gwamnatin Erdogan da kasancewa ta kama karya.