Sabani tsakanin Jonathan da Obasanjo | Siyasa | DW | 09.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sabani tsakanin Jonathan da Obasanjo

Kasa da tsawon makonni da zabukan dake tafe ana ci gaba da dauki ba dadi a tsakanin manyan dattawan kasar dake bisa mulki a Najeriya.

Da a dai ana masu kallo irin na shugabannin al'umma, sun ma kai ga cirar tutar shugabanci ga al'ummar kasa a lokuta dabam dabam.

To sai dai kuma sun koma da sana'ar wanke dan kanfansu a bainar jama'a a tsakanin manyan shugabannin kasar ta Najeriya dake rabe a bisa a zabe. Babu dai bata lokaci ga tsohon shugaban kasar Chief Olusegun Obasanjo da ya kalli tsabar idon babban yaron nasa, kuma shugaban dake ci yanzu, Goodluck Ebele Jonathan, yace masa ya kasa a cikin mulkin kasar, sannan ya gai komawa baya. Kalaman da kuma suka kai ga bude sabon babin rikici da ma fitar da datti a fili a tsakanin Chief Obasanjo da ya ambato cin hanci da ma rashawa, sannan kuma da matsalar rashin iya mulkin na kasa. A yayin kuma da aka ruwaito shi kansa Jonathan din ya maida martanin dake gugar zana da sunan yan tasha ga tsohon jagoran nasa.

Duk da cewar dai an saba ga batun rikici a tsakanin bangarori dabam dabam dake mulki a cikin kasar ta Najeriya, sabon yakin na Obasanjo da Jonathan dai tuni ya dauki hankali cikin kasar, inda ake masa kallon ba sabun ba, tare da raba raba kan 'yan kasar a tsakanin masu tunanin ya dace da kuma masu yi masa kallon ya saba da tunani na hankali.

Alhaji Tanko Yakasai dai na zaman tsohon mashawarcin siyasa ga tsohuwar gwamnatin Alhaji Shehu Shagari kuma a fadarsa buri irin na son rai ne ya kai ga dattawan mantawa da shekaru wajen tunkarar juna.

Olusegun Obasanjo

Chief Olusegun Obasanjo

Bukatar son rai ko kuma kokarin gyara kuskure dai, ana ta'allaka tsohon shugaban da alhaki kacokam ga rikidewar ta Jonathan ya zuwa babban dodon fadar gwamnatin kasar dake bawa kowa tsoro daga mai malafa mara takalmi na Bayelsa cikin tsawon kasa da shekaru takwas na mulkin nasa. Abun kuma da a fadar Dr. Emman Shehu, dake nazari bisa harkoki siyasar kasar ya sanya zama wajibi ga Obasanjo wanke suna dama kimarsa cikin kasar dake masa kallon laifi yanzu haka.

Abun jira a gani dai na zaman tasirin da fadan zai yi a cikin jam'iyyar PDP da shugabannin biyu kewa biyayya da ma kasar ta Najeriya da suke neman juya akalarta daga gefe.

Sauti da bidiyo akan labarin