1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabani game da taimako ga yankin Arewa Maso Gabas

December 30, 2013

Gwamnatin Najeriya ta maida mrtani a game da kace-nace kan yawan taimako ga yankin Arewa Maso Gabas, tare da cewar ba a fahimci gaskiyar al'amarin bane.

https://p.dw.com/p/1Aibc
Hoto: NICHOLAS KAMM/AFP/Getty Images

A matakinta na maida murtani kan cece-kucen day a biyo bayan kasafta Naira bilyan biyu da ta yi domin kai dauki ga jihohin da ke arewa maso gabashin Najeriyar, gwamnatin kasar tace shirin talafawa jihohin yanki na shekaru biyar take da shi don haka wannan soma tabi ne kawai.

To cece kucen day a biyo bayan kasafta Naira bilyan biyu da gwamnatrin Najeriyar ta yi ga jihohin shida da ke yankin arewa maso gab ashin Najeriya, da day a biyo bayan bankado cewar gwamnati ta samar da irin wannan tallafi ga yankin Niger Delta har na Naira milyan dubu 114, day a sanya su cewa wannan cin zarafi ne ba wai tallafi ba.

Wannan ya sanya gwamnatin Najeriyar cewa akwai rashin fahimtar manufarta a kan wannan shiri, domin kuwa a tsanake take son nazarin bukatun wannan yankin da ke ci gaba da shan hare-haren bama-bamai na sojoji da ma kungiyar Ahlu Sunnah Li Da'awatti Waljihad wato Boko Haram, wanda ya durkusar da daukacin tattalin arzikin yankin. Dr Yarima Lawal Ngama shine ministan kasa a ma'aikatar kula da harkokin kudi ta Najeriya.

Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima,
Hoto: DW

‘'Wannan kudi bilyan biyu da aka sa ba wai kudi ne da za'a gingina makarantun da suka kokone ko kuma wasu abubuwa manya-manya muhimmai ba, A'a wannan kudi ne da za'a talafawa su mutanen da ke zaune a wadan nan jihohi musamman ma samari wanda basu da aikin yi, da kuma mata wanda basu da jarri da sauransu. To amma da mutanen suka ga wannan bilyan biyu an sa a kasafin kudi sai suka dauka wannan kwata kwatra shine abinda gwamnati zata kasha, har ma suka rinka wata tsokana da gwada wasu kudade da aka ware a wasu wurare. To kaga wannan, to kaga wannan tsokana ce domin a ingiza mutane''

Duk da kokarin kare kai da gwamnati ta yi a kan wannan batu da ya kara jefa zargin wanzuwar yayan mowa da na bowa a yadda ake tafiyar da al'ammura a Najeriyar, da alamun an kama hanyar kwasan yan kalllo a tsakanin bangaren zartaswar da na majalisa, musamman ga wakilan talakawan yankin arewa maso gabashin Najeriyar da suke cewa sai fa sun bi dididgin wannan Magana a majalisar. Ko wannan na nufi basu haklara ba kenan? Hon. Aliyu Ibrahim Gebi na majalisar wakilan Najeriya na cikin masu wannan alwashi.

Dr. Yarima Lawal Ngama, karamin minista a ma'aikatar kudin Najeriya
Hoto: DW/U. A. Idris

‘'Ka tsaya mu dawo daga hutu kaga ikon Allah, mutanenmu nawa ake kashewa sannan ace wai mu yi shiru, yankinmu fa jihohi shida ace an dauki naira bilyan biyu an bamu Kaman masu bara, in in muka yi shiru muka karbi wannan kudin da mu da na sama da mu ai azabar Allah ya sauka.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris

Edita: Umaru Aliyu