1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Rashin albashi ga 'yan sanda

November 18, 2020

A Najeriyar sababbin 'yan sandan da aka dauka na kokawa kan yadda suka shafe sama da watanni 10 suna aiki ba tare da karbar ko kwandala da sunan albashi ba.

https://p.dw.com/p/3lWaV
Symbolbild | Nigeria | SWAT
'Yan sandan Najeriya na kokawa kan karancin albashiHoto: AFP/Y. Chiba

Sababbin jami'an 'yan sandan sun ce rashin samun albashin tsawon watanni, shi ke tilasta musu cin bashi domin su je wajen aiki da ma karbar na  goro a hannun jama'a a wani lokaci. Da dama dai daga cikin sababbin 'yan sandan, na korafi ne saboda rashin biyan su kudin albashi, yayin da kuma  iyayensu ke ci gaba da nuna takaici a kan hakan. Tuni dai ake ta nuna 'yar yatsa ga Najeriyar kan sako-sakon da ake zargin tana yi ga jami'an tsaro musamman a irin wannan lokaci da Najeriyar ke fuskantar matsalolin tsaro, kama daga garkuwa da mutane da kuma ayyukan masu tayar da kayar baya.

DW ta yi kokarin tuntubar hukumomin 'yan sandan na Najeriya kan wannan batu, ba tare da haka ta cimma ruwa ba. Duk da irin kalubalen da sababbin jami'an ‘yan sandan ke fuskanta na rashin albashi, na masu cike da fatan ranar da gwamnatin kasar za ta fara biyan su albashin aikin tsawon watanni da suka yi, domin kara  matsa kaimi ga tunkarar rashin tsaron da ya addabi Najeriyar.