1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ruwan kwallaye a Bundesliga da Premier

October 5, 2020

A wannan Litinin din ake rufe kasuwar cinikin 'yan wasa a nahiyar Turai. Hukumar Kwallon kafa ta duniya FIFA ta gudanar da babban taronta karo na 70, wanne nasararori ko kalubale aka fuskanta?

https://p.dw.com/p/3jSJt
UEFA Champions League | RB Leipzig vs Lyon
Hoto: Getty Images/Bongarts/C. Kaspar-Bartke

A wannan Litinin din ake rufe kasuwar cinikin 'yan wasa a tsakanin kungiyoyin nahiyar Turai. Tuni dai kungiyoyin kwallon kafar na nahiyar Turai suka fara kokarin karkare cininkin 'yan wasan da suke da bukata. Annobar cutar corona da duniya ta tsinci kanta a ciki, ta taka gagarumar rawa wajen cinikin 'yan wasan a bana, inda kungiyoyin ke taka-tsan-tsan wajen sanya hannu kan yarjejeniya da sabbin 'yan wasa.

UEFA Champions League | RB Leipzig vs Lyon
Hoto: Getty Images/AFP/R. Hartmann

Daga cikin 'yan wasan da ake sa ran za a rufe kasuwar da cinikinsu akwai Douglas Costa da ake sa ran zai sake dawo wa kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich da kuma Memphis Depay da zai tafi Barcelona. Haka ma kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ana sa ran za ta kammala cinikin Alex Telles baya ga tattaunawar da take da dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund wato Jadon Sancho da kuma dan wasan gaba na Uruguay da ba shi da kungiya wato Edinson Cavani.

Karawa tsakanin Chelsea da Liverpool
Karawa tsakanin Chelsea da LiverpoolHoto: Jason Cairnduff/AFP/Getty Images

Idan muka leka gasar Premier League ta kasar Ingila kuwa, a mako na hudu na kakar wasannin ta bana, can ma an yi ruwan kwallayen, inda Chelsea ta lallasa Creastal Palace da ci 4-0 Everton ta samu nasarar a kan Brighton da ci 4-2 yayin da Arsenal ta samu nasara da ci 2-0 a fafatawa tsakaninta da Sheff United. Inda aka fi ruwan kwallaye shi ne karawar da aka yi tsakanin Manchester United da Totenham, inda Totenham din ta bi Mancherster United har gida ta lallasa ta da ci 6-1, ita kuwa Leverpool ta kwashi kashinta a hannu da ci 7-2, a karawar da suka yi da Astonvilla. A yanzu haka dai, Everton ke saman tebur din da maki 12 yayin da Aston villa da Lester da Arsernal da Lever Pool ke biye mata da maki tara-tara a mastayi na biyu zuwa na biyar.