1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin biyan diyya ga wadanda rusau ya rutsa da su a Konkary

March 29, 2021

Hukumomi a kasar Gini suna ci gaba da rusa kantunan sayar da abinci da gidaje da nufin fadada hanya. Tuni ma al'ummar kasar suka fara korafin cewa ana raba su da matsugunansu ba tare da biyan su diyya ba.

https://p.dw.com/p/3rKzN
Tun gabanin matakin rusaun, masu zanga-zanga a lokacin zabe sun lalata wurare da dama
Tun gabanin matakin rusaun, masu zanga-zanga a lokacin zabe sun lalata wurare da damaHoto: John Wessels/AFP

Ba abin da ake gani a manyan titunan Konakry illa yadda katafila ke ruguje wuraren cin abinci da shaguna da gidajen jama'a, duk kuma domin a sami damar aiwatar da ayyukan raya kasa. Hasali ma dai gwamnatin Gini ta ce tana wannan yunkuri ne domin fadada hanyoyin babban birnin kasarta tare da kawata wadannan wurare da gine-ginen da suka dace.

Ma'aikatar gidaje tare da hadin gwiwar gwamnan birnin Konakry ne ke jagorantar aikin na rusau, kuma suka ce wannan somin tabi ne domin za su fadada aikin nasu zuwa ga dukkanin kauyukan da ke kewayen birnin na Konakry. Ko da kantomar garin Coyah da ke wajen kilomita 50 da babban birnin kasar ta Gini, sai da ya danganta yunkurin nasu da neman kwato filayen gwamnati da jama'a suka mamaye tare da mallaka ba bisa ka'ida ba. A lokacin da yake bayani, Aziz Diop ya ce kwalliyarsu ta fara biyan kudin sabulu domin filaye da aka riga aka dawo da su karkashin ikon gwamnati na da yawa.

Karin bayani:Gini: Kokarin tsabtace bakin kogin Konakry

"Ministan babban birnin da tsarin yankuna ya ziyarci garin Coyah kuma ya fatattaki wadanda suke zaune a gidaje ba bisa doka ba, ciki har da kwato filiye mallakin gwamnati. A cikin unguwar Sambaya, an rusa duk abubuwan da ya kamata don rage cunkoson ababen hawa. An saki hakkin-hanya domin dawo da tsarin zirga-zirgar motoci. Muna matukar farin ciki da aikin rusau. Wannan ana yi ne ba don adawa da kowa ba, muna yi ne domin kyautatawa da kuma samar da kyakkyawan yanayin rayuwar mutanen kasar nan."

Kasar Gini na da unguwanni na marasa galihu a babban birninta wato Konakry
Kasar Gini na da unguwanni na marasa galihu a babban birninta wato KonakryHoto: John Wessels/AFP

Unguwanni da dama wannan aiki ya shafa kama daga Kaloun, a tsakiyar garin Konakry, zuwa Dubréka da Coyah da ke wajen garin babban birnin kasar. Sai dai wasu 'yan kasuwa sun gwammace kwashe nasu ya nasu, tun ma kafin motocin rusau su iso.

Karin bayani: Shara ta kashe mutane takwas a Konakry

Gidajen cin abinci da kananan 'yan kasuwa a yankunan ne wannan rusau ya fi shafa. Mohamed Bangoura wanda na daya daga cikin 'yan kasuwa da aka rusa shagunansu gaba daya, ya ce ya rasa dukkan kwastomominsa.

"Wata rana da karfe 5 na yamma suka zo suka shafa wa shagunanmu alama a bakin hanya. Kashegari mutane suka fara wargaza kantinsu da kansu saboda idan sun zo za mu raina kanmu. Na rasa duk kwastomomina saboda ba ni da shago yanzu. A nan ne nake baza hajata yanzu, amma kwastomomin da ke wucewa ba sa ganina. Na rasa kashi 60 cikin 100 na abokin cinikina."

Wannan ba shi ne karon farko da gwamnati ke rusau a Konakry ba, amma ba ya hana wadanda ta taba gidajensu sake komawa inda aka kore su. Sai dai a wannan karon, rusau din ta ta'azzara kuma ta shafi wurare da dama ciki har ma da wadanda gwamnati ta mallaka.