Shara ta kashe mutane takwas a Konakry | Labarai | DW | 22.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shara ta kashe mutane takwas a Konakry

Mutane akalla takwas ne suka halaka a yayin da wasu da dama suka ji rauni a wata unguwar birnin Konakry babban birnin kasar Guinea a sakamakon zarftarewar wata dalar bola, biyo bayan wasu ruwan sama masu yawa.

Mutane akalla takwas ne suka halaka a yayin da wasu da dama suka ji rauni a wata unguwar 'yan rabbana ka wadata mu ta kewayen birnin Konakry babban birnin kasar Guine a sakamakon zarftarewar wata dalar bola, biyo bayan wasu ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka share mako daya ana zubawa a birnin. 

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya rawaito cewa da idanunsa ya ga lokacin da aka zakulo gawarwaki biyar da suka hada da na wasu kananan yara biyu daga karkashin bolar a unguwar yah ayyuhannasu ta Hamdallai.

Kwamishinan hukumar kula da harakokin tsaro a birnin na Konakry ya bayyana cewa dalar bolar ta rikito ne kan wasu gidaje uku, kuma yanzu haka jami'an ceto na can na kokarin zagulo wasu mutanen a karkashin gine-ginen da aka tabbatar na raye ya zuwa yanzu.