1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rouhani: Sai an cire takunkumi za mu tattauna

Abdullahi Tanko Bala
August 27, 2019

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya sassauto akan yiwuwar ganawarsa da Donald Trump, yana mai cewa dole ne shugaban na Amirka ya fara dage takunkumin da ya kakabawa Iran

https://p.dw.com/p/3OZkY
Bildkombo - Trump und Rohani

Sauyin matsayin na Hassan Rouhani ya zo ne kwana guda bayan da a jiya litinin Trump yace akwai haske mai karfi cewa shugabannin biyu za su gana kan takkadamar su ta nukiliya, bayan tsoma baki na ba zata ba da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi kan batun a taron kolin kasashe bakwai masu karfin tattalin arziki na duniya domin jawo hankalin Amirka da Iran su fahimci juna bayan tsawon shekaru suna zaman doya da manja.

Macron yace yana fata cikin 'yan makonni Trump da Rouhani za su hadu domin ceto yarjejeniyar nukiliyar da Iran ta cimma da manyan kasashen duniya a shekarar 2015 wadda kuma Amirka ta yi gaban kanta wajen ficewa daga cikin sa a bara.