Robert Mugabe ya rasu | Labarai | DW | 06.09.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Robert Mugabe ya rasu

Tsohon shugaban kasar Zimbabuwe wanda ya jagoranci kasar zuwa tafarkin 'yanci ya rasu.

An sanar da mutuwar tsohon shugaba Robert Mugaben ne yana mai shekaru 95 a duniya.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Shugaba Emmerson Mnangagwa na kasar ya bayyana kaduwa da mutuwar tsohon shugaban.

Robert Mugabe ya zama Firai Ministan kasar daga shekarar 1980 zuwa shekara ta 1987.

Ya kuma zarce a matsayin shugaban kasa a shekarar 1987 da kuma ya rike har zuwa shekarar 2017 da sojoji suka hambarar da mulkin nasa.

Marigayin ne dai ya jagoranci gwagwarmayar da ta kai Zimbabuwe ga samun 'yancin kai daga Turawan Birtaniya.

Ya kuma rasu ne a wani asibiti da ke kasar Singapore bayan jiyya da ya yi a can.