Rikicin Siriya zai mamaye taron G20 | Siyasa | DW | 05.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikicin Siriya zai mamaye taron G20

Taron ƙasashe masu arziƙin masana'antu na G20 ya zo daura da taƙaddamar da ƙasashen ke yi kan matakin ɗauka a Siriya abin da ake gani zai ja hankali, a taron da ya kamata ya yi nazarin tattalin arziƙin duniya

Barazanar ɗaukar matakin soji a kan Siriya na ci gaba da jan hankalin shugabanin duniya, a daidai lokacin da ƙasashe masu arziƙin masana'antu na G 20 ke taro a Rasha, domin tattauna batutuwan tattalin arziƙi da yadda suke tasiri kan marasa aikin yi da kuma masu fama da talauci musamman a ƙasashe masu tasowa. Sai dai duk da cewa masu rajin kare hakkin bil adama na kira ga shugabanin su mayar da hankali ga batutuwan da suka haɗa da matsalar cin hanci da rashawa, da kamfanonin dake ƙin biyan haraji, makomar Siriya ya kasance mafi mahimmanci kan ajandar taron.

Shugabanin da ke kan gaba a rikicin Siriyan zasu kasance a ɗaki guda na tsawon yini biyu a St Petersburg, waɗanda daga cikinsu akwai shugaba Barack Obama na Amirka, Vladimir Putin na Rasha, Francois Hollance na Faransa, Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Monn, shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da kuma Prince Saun Al Faisal al Saud na Saudiyya. Sanin kowa ne ko banda Siriya, dama can Obama da Putin na da jiƙaƙƙiya tsakaninsu musamman saboda matakin Rasha na ɓoye Edward Snowden wanda ya kwarmato bayanan sirrin Amirka.

Organisation for Economic Co-operation and Development (OECD) Secretary-General Angel Gurria (L) presents members of the delegation to Russia's President Vladimir Putin during a meeting at the Kremlin in Moscow, February 14, 2013. REUTERS/Maxim Shemetov (RUSSIA - Tags: POLITICS BUSINES

Ministocin ƙasashen G20 tare da shugaba Putin

Mahimmancin taron G 20 ga ƙasashe masu tasowa

Kasancewar ƙasashen na G20 na wakiltar kusan kashi biyu cikin uku na yawan al'ummar duniya ne, da kuma kashi 85 na abin da ƙasashe ke samu kowace shekara da ma dakarun soji, akan gudanar da wannan taron ne da burin ganin cewa an daidaita yadda ake rabon tattalin arziƙin duniya saboda waɗanda ke can ƙasa su samu, amma kuma a wannan karon mai yiwuwa ba zai cimma wannan buri ba. Ko da shi ke a ganawar da ta yi da manema labari bayan an buɗe taron shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce wakilan ƙasashen na G20 za su yi nazarin tattalin arziƙin duniya da fannonin da ke buƙatar a inganta su

"A ajandarmu akwai shirin St Petersburg wanda ya karkata ga tabbatar da ci-gaban tattalin arziƙin duniya, wanda ba abin da ƙasa ke samu kowace shekara zai yi la'akari da shi kaɗai ba, har ma da yadda ake tsara kuɗin da ƙasa take kashewa a kanta. Zamu ɗauki mataki mai mahimmanci a fuskar daidaita kasuwannin hada-hadar kuɗi da kuma batun haraji. Na farko dai za mu yi musayar bayanai dangane da waɗanda ke ɓoye kuɗaɗensu su ƙi biyan haraji kuma wannan zai kasance mataki na bai ɗaya a tsakanin ƙasashen na G20 ba tare da an nunawa kowa banbanci ba, na biyu kuma zamu duba waɗannan kamfanonin waɗanda sukan kaucewa biyan harajin baki ɗaya, su zaɓi tanade-tanaden da zasu mutunta su bar sauran ta yadda a ƙarshe ba za su biya ko sisi ba."

Bundeskanzlerin Angela Merkel und der amerikanische Präsident Barack Obama unterhalten sich vor Beginn des G 20 Gipfels in Cannes bei einem bilateralen Treffen. Am 03. und 04.11.2011 treffen dann die Staats- und Regierungschefs der führenden Volkswirtschaften der Welt (G20) zu ihrem diesjährigen Gipfel zusammen. Foto: Guido Bergmann

Angela Merkel da Barack Obama

Tasirin rikicin Siriya

Duk da cewa shugabar gwamnatin na Jamus bata ambaci Siriya ba, rikicin ya ɗauki salon da shugabanin manyan ƙasashen ke gani zai yi tasiri sosai kan tsaro da tattalin arziƙin ƙasashensu, Tarayyar Turai a nata ɓangaren tayi tir da amfani da makamai masu guban da aka yi amfani da su a Siriyar, amma kuma ta ce mai yiwuwa babu harin da za'a kai kan ƙasar domin a ganinta, sulhu ta hanyar diplomasiyya ce kaɗai maslaha ga rikicin na tsawon shekaru biyu da rabi yanzu.

Shugaban Majalisar zartarwar ƙungiyar Tarayyar Turai Herman Van Rompuy tare da shugaban ƙungiyar Jose Manuel Barosso ne suka bayyana hakan a matsayin inda Turai ta dosa, abin da kuma ya nuna akwai saɓanin ra'ayi da inda Amirka ta dosa, sai dai Shugaba Barack Obama na shirin samun goyon bayan majalisar ƙasarsa dan mayar da martani ga harin na makamai masu guba. Ministan harkokin wajen Jamus ya shawarci da a baiwa kotun hukunta laifukan yaƙi hurumin gudanar da bincike kan wannan batu

BRICS' heads of state, from left, Brazil's President Dilma Rousseff, Russia's President Vladimir Putin, India's Prime Minister Manmohan Singh, China's President Hu Jintao and South Africa's President Jacob Zuma pose for a group photo at the G-20 Summit in Los Cabos, Mexico, Monday, June 18, 2012. (Foto:Andres Leighton/AP/dapd)

Shugabanin ƙasashen BRICS

Rawar ƙasashe masu samun ci-gaban masana'antu

"Ana fara taron na ƙasashen G20 daura da taƙaddamar da ƙasashen ke yi kan matakin ɗauka a Siriya shi ya sa Siriya ya kasance batu mai mahimmanci, shi ya sa wajen tattaunawarmu na sake gabatar da buƙatar cewa kwamitin sulhu ya fitar da ƙudurin da zai bai wa kotun ƙasa da ƙasa na hukunta manyan laifukan yaƙi izinin gudanar da bincike mai zaman kanshi

A shari ɗaya kuma akwai batun ƙasashen na masu samun ci-gaban masana'antu na BRIC waɗanda suka haɗa da Brazil da Rasha da Indiya da China waɗanda ke ƙoƙarin daidaita takardun kuɗinsu waɗanda darajar ta fara faɗuwa bayan da Amirka ta ƙara kuɗin ruwa kan basussukanta, a baya dai sun ƙaddamar da wani shiri na samar da bakin raya ƙasa ta haɗin gwiwa a tsakaninsu ko da shi ke ba su tantance inda bankin zai kasance da ma nawa kowace ƙasa za ta bayar ba, a wannan karon ne ake sa ran Vladimir Putin na Rasha zai sanar da wasu daga cikin abubuwan da suka cimma.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin