1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Libiya na lakume rayuka

April 8, 2019

Akalla mutum 35 ne suka salwanta a Tripoli na kasar Libiya, a sabon rikicin nan da ya barke tsakanin kwamandan askarawan kasar Khalifa Haftar da Fayez al- Serraj da ke rike da iko.

https://p.dw.com/p/3GSky
Libyen Mitglieder der National Army LNA in Bengasi
Hoto: Reuters/E. O. Al-Fetori

Rahotannin da ke fitowa daga Tripoli babban brinin kasar Libiya, na cewa wasu jiragen yaki sun kai hari ta sama a kan babban filin jirage na birnin.

Wasu majiyoyi daga filin jiragen, sun ce babu wanda ya dauki alhakin hari wanda ke zuwa yayin da fada tsakanin kwamandan asakarawan kasar Khalifa Haftar da kuma Fayyez al-serraj mai rike iko ke kara kazanta.

Bayanai na cewa akalla mutum 35 aka tabbatar da salwantarsu da safiyar wannan Litinin, wasu sama da 80 kuwa suka jikkata.

A baya dai alkaluman wadanda suka mutu 21 ne kafin fitowar sabbin alkaluma a ranar Litinin, da kuma suka tabbatar da salwantar wasu daga cikin dakaru magoya bayan Khalifa Haftar.

A ranar Alhamis na makon jiya ne kwamanda Haftar, ya bayar da umurnin dannawar sojojinsa don kwato fadar gwamnatin kasar daga bangaren da kasashen duniya suka amince da shugabancinsa a Libiyar.

Sashen kula da harkokin jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a kasar, ya ce akalla mutum 2,800 ne suka rasa muhalli a birnin na Tarabulus, ya zuwa yanzu.