Rikicin kabilanci ya barke a Adamawa | Labarai | DW | 24.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin kabilanci ya barke a Adamawa

Rahotannin da ke fitowa daga a jihar Adamawa da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya na cewa, mutane da dama ne ake fargabar sun mutu sakamakon barkewar rigima tsakanin 'yan kabilun Bachama da Fulani a yankin Gereng.

Ana dai zargin cewar fulani makiyaya ne suka afkawa yankin, a wani abin da aka ce hari ne na fansa, bayan wata rigima da ta shiga tsakanin al'umomin biyu a kwanakin baya.

Wani maharbi mai suna Aliyu Kaura, ya shaidawa wakilinmu na Yola Muntaqa Ahiwa cewar lamarin ya kazanta saboda ya kai ga kone-konen gidaje da dama.

a inda ya kara da cewar dama a kwai wata jikakkiya a kwance a tsakanin kabilun biyu kana kuma a kwai yuwuwar cewar an kashe D.P.O a yankin da yaje kokarin saisaita rigimar.

Rikicin wanda ya barke tun a ranar a sabar da tsakar dare ya lakume rayukan mutane da dama sai dai ya zuwa yanzu babu wasu cikakkun bayanan binciken karin bayani daga jami'an tsaro a karamar hukumar Girei a cikin jihar ta Adamawa a Najeriya.