Rikicin Girka ya mamaye taron G7 | Labarai | DW | 28.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Girka ya mamaye taron G7

Kasashe masu manyan masana'antu na G7 na taro a Jamus domin lalubo hanyoyin inganta arzikin kasashen duniya.

Shugabar Asusun ba da Lamuni na Duniya IMF, Christine Lagarde na ganin cewa akwai sauran aiki a tattaunawar da ake yi dan taimakawa Girka da kudade domin ceto ta daga rikicin kudin da ta shiga yanzu, kuma wannan ya kasance haka duk da irin aikin da aka yi a makonnin da suka gabata. Shugabar Asusun Bada Lamunin ta bayyana hakan ne a taron kasashe masu manyan masana'antu na G7 da ke gudana a birnin Dresden na nan Jamus da zuman nemo hanyoyin bunkasa tattalin arzikin kasashen duniya, sai dai batun Girka ne ya mamaye taron.

Jamus ce ke rike mukamin shugabancin karba-karba na kasashen na G7 kuma da ma ministan kudin kasar Wolfgang Schauble ya gayyace takwarorinsa daga Birtaniya, Kanada da Faransa da Italiya da Japan da Amirka domin su duba mahimman batutuwan da za su kawo cigaba kamar halin da tattalin arzikin duniya ke ciki, da daidaita dokokin kudi da matsalar kin biyan kudin haraji da ma matakan toshe hanyoyin da kungiyoyin ta'adda ke samun kudaden shiga