1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Rikici kan mafi karancin albashi

May 22, 2024

A wani abun da ke zaman alamun rikici tsakanin gwamnatin Tarayyar Najeriya da ma'aikatan kasar, manyan kungiyoyin kodagon kasar sun ce a kai sabon mafi karancin albashin kasar kasuwa.

https://p.dw.com/p/4gA4a
Najeriya | NLC | TUC | Bola Ahmed Tinubu | Albashi
Shugaban Najeriya Bola Ahmed TinubuHoto: Gbemiga Olamikan/AP/dpa/picture alliance

Duk da cewar dai suna shirin ci gaba da tattaunawa dai, daga dukkan alamu babu sassauci a tsakanin gwamnatin Tarayyar Najeriyar da kungiyoyin kodagon kasar kan batun mafi karancin albashin. Tuni dai NLC ta sa kafa ta shure  sabon tayin Naira dubu 54 da gwamnatin kasar ta yi, wanda ke zaman na biyu tun bayan fara tattaunawa tsakanin bangarorin biyu. Korafin rashin kudi ko kuma wadaka da dukiyar al'umma, 'yan kodagon dai na neman Naira dubu 615 a matsayin mafi karancin albashin.

Najeriya | NLC | TUC | Bola Ahmed Tinubu | Albashi
Kungiyoyin kodogon Najeriya, sun jima suna ikirarin yin fafutuka domin ma'aikatan kasarHoto: Uwais/DW

Gwamnati dai na kukan rashin kudi, inda masu mulkin kasar dai suka dau hanyar cin bashi da kokarin kara haraji a cikin fatan iya kai wa ya zuwa sauke nauyi ga shugaban da ke cika shekararsa ta farko a mulkin kuma hankalinsa ke kara karkata zuwa neman hanyar burge masu zabe a Najeriyar ta hanyar karin albashin. Koma ya zuwa ina masu mulkin suke tunanin lallashi ga kodagon yana iya kai wa ya zuwa ga bukata dai, daga dukkan alamu suna da sauran aiki a turjiyar da ke barazanar rikidewa ya zuwa babban rikici.

Najeriya | Talauci | Tsadar Rayuwa
Talauci da tsadar rayuwa na addabar al'umma a NajeriyaHoto: KOLA SULAIMON/AFP/Getty Images

'Yan kodagon dai sun ce Abujar na da zabi ta amince da bukatunsu ya zuwa karshen watan Mayun nan, ko kuma ta fuskanci yajin aikin sai baba-ta-gani. Ko bayan jan ido na masu kodagon kasar dai, akwai tsoron karuwar talaucin da ke cikin kasar na iya janyo rikici mai girma a cikin yajin aikin ma'aikatan kasar.  Dakta Isa Abdullahi dai na zaman kwararre kan tattalin arzikin kasar, kuma yace Abujar na da bukatar aiki da hankali cikin daidaiton lamura a cikin kasar a halin yanzu. Abun jira a gani dai na zaman yadda take shirin kayawa a cikin kasar da masu mulkin ke kara shiga rudu, a kokarin tara kudin yin mulki da masu kodagon da ke fadin a gyara rayuwa.