Rikici a kasuwar Alaba International da ke jihar Legas | Labarai | DW | 19.10.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikici a kasuwar Alaba International da ke jihar Legas

A jihar Legas da ke kudancin Najeriya an sami barkewar rikici a kasuwar nan ta Alaba International tsakain wasu 'yan kasuwa da matasan nan 'yan Agbero masu karbar kudade da sunan Haraji.

Wannan lamari ya haifar da tsaiko kan sha'anin kasuwanci a kasuwar, inda mutane da dama suka gaza bude shagunanu, sai dai ya zuwa yanzu ba wani labari da aka samu na jikkata ko asarar rai.

Wakilimu da ke jihar Legas Mansur Bala Bello ya ce wannan rikici bai shafi kasuwar nan ta Alaba Rago ba wadda galibin masu kasuwanci a wajen Hausawa ne. 

Shi ma dai sarkin Kasuwar ta Alaba Rago Alhaji Muhammad Nagoggo Sokoto ya tabbatar da wannan labari a zantawarsa da DW.