Rex Tillerson zai kai ziyara kasashen Afirka
March 2, 2018Talla
Ziyarar da ke zama ta farko a wannan nahiya tun bayan da Shugaba Donald Trump ya hau karagar mulki.
Tillerson zai ziyarci manyan biranen kasashen Chadi da Djibouti da Habasha da Kenya da Najeriya, a ziyarar da zai kai tsakanin ranakun shida zuwa 13 ga watan nan na Maris kamar yadda Heather Nauert da ke magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen na Amirka ta bayyana a ranar Alhamis.
Wannan ziyara dai ta Tillerson na zuwa ne bayan da mai gidansa Trump a watan Janairu ya bayyana kasashen na Afirka a matsayin kofar shadda, ana kuma sa ran a lokacin ziyarar ya gana da shugabanni na kasashen da shugabanni a kungiyar AU inda za su mayar da hankali kan batutuwa da suka shafi tsaro da kasuwanci da shugabanci nagari.