Rayuka sun salwanta a wani rikicin makiyaya da manoma a Adamawar Najeriya | Labarai | DW | 03.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rayuka sun salwanta a wani rikicin makiyaya da manoma a Adamawar Najeriya

Akalla mutane 10 suka mutu sannan kimanin dubu 40 sun tsere daga kauyen Kadamun na karamar hukumar Demsa.

Rahotanni daga kudancin jihar Adamawa a Najeriya na cewa rayuka da dama ne suka salwanta sakamakon wani harin da ake zargin makiyaya da afka wa manoman yankin Kadamun da ke cikin karamar hukumar Demsa.

Alkaluman farko dai sun ce kimanin mutane goma ne aka kashe, sai dai 'yan siyasa da ma mazauna yankin sun ce sun zarta hakan. Sannan kimanin mutane dubu 40 ne suka tsere daga kauyen da kewaye.

Wani da ya shaida abin da ya faru ya fada wa wakilinmu na Adamawa Muntaqa Ahiwa cewa yawan wadanda suka mutun ya zarta mutum goma kana ana kai gawarwaki cikin gari.

Tuni jami'an tsaron Adamawan suka tabbatar da faruwar lamarin, wanda ya auku daga daren Asabar zuwa Litinin.