Rashin bin doka da oda a Libiya
October 23, 2013Shekaru biyu bayan gagarumar rawar da ta taka wajen rugurguza dakarun sojin Libiya, kungiyar NATO ta fara shirye-shiryen bada horo ga sabuwar rundunar sojin kasar, a daidai lokacin da matsalar tsaron kasar ta Libiya ta fara tsallakawa zuwa ketare.
A cikin wata sanarwa da ta gabatar a yayin taron jakadun kasashen kungiyar a birnin Brüssels, kungiyar ta kafa kwamati da zai tsara taswirar kan hanyar da za ta kai ga farfado da dakarun sojan kasar ta Libiya, don amsa rokon da Firaiministan kasar Ali Zaidani ya yi wa kungiyar, bayan da kasarsa ta fara zama tungar 'yan ta'addan da ke barazana ga tsaron duniya.
Ilyas Albaruni, kakakin Firaiministan na Libiya ya danganta matakin da kasar tasa ta dauka na sake gayyato NATO da wani mataki da ya zama na dole, don magance zaman kara zube da kasar ta yi shekaru biyu cikinsa.
"Batun tsaro, shi ne babban batun da muka sa gaba. Ba mu da niyar ba wa kungiyar NATO sansani a Libiya. Akwai yarjejeniyar cudeni in cudeka ta tsaro tsakaninmu da su, don haka muke fata za su sake taimaka mana don tunkarar wannan kalubale."
Sabon salon mulkin mallaka
Wasu mayakan sa kai na kungiyoyin 'yan tawayen kasar, sun nuna adawarsu da wannan mataki da gwamnatin Ali Zaidanin ta dauka, suna masu cewa wannan mataki zai dawo da tsarin mulkin mallaka ne, da zai cusawa sojin kasar ta Libiya akidar kare bukatun kasashen iyayen gijinsu fiye da ba wa al'ummar kasar Libiya kariya.
"Mu mutanan garin Zawiya fafutukarmu ta kare hakkin 'yan kasa ne. Ba za mu lamunta da mayar Libiya ta zama sansanin dakarun kasashen ketare ba. Yanzu shin kakagidan da suka yi mana a rijiyoyinmu na man fetir, da kuma makudan kudaden da suke kwasa da sunan sake gina Libiya bai ishesu ba? Muna son ganin an gina sojojin Libiya kan akidar kishin kasa, da kaunar ilahirin mutanenta."
Rashin bin doka da oda ya zama ruwan dare
Tun bayan karya gwamnatin Kanal Gaddafi shekaru biyun da suka gabata dai kasar ta Libiya take fama da matsalolin tsaro kama daga kisan dauki dai-dai da ake wa manyan jami'an tsaro da hafsoshin sojin kasar, gami da kai hare-hare kan ofisoshin kasashen Yamma, yadda a bara aka kone jakadan Amirka a ofishin jakadancin kasarsa dake Libiya. Sannan a baya bayan nan wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da shi kansa Firaiminista Ali Zaidani.
Kamar yadda masharhanta ke gani, fakewar da 'yan tawayen kasar Mali da dakarun sojin Faransa suka tarwatsa a cikin kasar ta Libiya, da kuma tururuwar da bakin hauren dake neman tsallakawa zuwa Turai ke yi a kasar ta Libiya, na daga cikin dalilan da ke nuni da matukar bukatar samar da gogaggun dakarun soji a Libiyar don kiyaye iyakokinta da kasashe yadda ya kamata.
Mawallafi: Mahmud Yaya Azare
Edita: Mohammad Nasiru Awal