Rasha: 'Yan sanda sun kama matar Navalny
January 31, 2021Talla
Masu aiko da rahotanni suka ce an kama Yulia Navalnaya ce tare da sama da mutane dubu biyu da suka fito zanga-zangar ta yau wadda ke gudana a sassa daban-daban na kasar.
Gabannin fara zanga-zangar dai hukumomi sun sanar da haramta amma kuma magoya bayan Navalny din suka yi watsi da wannan kira da mahukunatn na Kremlin suka yi.
Tuni dai kasashen duniya ciki kuwa har da Amurka suka nuna rashin jin dadinsu kan abin da suka kira amfani da karfin iko kan wanda ke adawa da gwamnatin da Vladmir Putin ke jagoranta.