1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami'an tsaro na binciken 'yan adawa a Rasha

Zulaiha Abubakar MNA
September 12, 2019

Jagoran adawa a Rasha Alexei Navalny ya dora alhakin binciken da 'yan sanda ke gudanarwa a ofisoshinsa kan gwamnati, bayan ya zargi jam'iyya mai mulki da huce takaicin rashin nasarar zaben da ya gudana.

https://p.dw.com/p/3PTvT
Russland Leonid Volkov
Hoto: picture-alliance/dpa/Sputnik/E. Odinokov

A wannan rana ta Alhamis 'yan sanda suka fara binciken gidaje da guraren sana'o'in magoya bayan jagoran adawar kaar Rasha, Alexei Navalny, da kuma wadanda suka bi umarninsa na zuba kuri'un da za su kawo karshen jam'iyya mai mulki ta shugaban kasar Vladmir Putin a zaben da ya gudana a ranar Lahadin da ta gabata.

Wannan samame ya biyo bayan binciken da hukumar yaki da cin hancin kasar ta Rasha ta kaddamar kan Navalny da masu hannu da shunin da ke mara masa baya a siyasance.