1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta yi yunkurin yi wa OPCW kutse.

Abdullahi Tanko Bala
October 4, 2018

Bayan Birtaniya da Australia sun zargi Moscow da yi wa kasashen duniya kutse ta Internet, kasar Netherland ta bankado yunkurin yin kutse kan hukumar binciken makamai masu guba, sai dai Rasha ta musanta zargin.

https://p.dw.com/p/35zJt
Niederlande PK zu Russische Cyber-Spione des Landes verwiesen
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Dutch Defense Ministry

Babbar jami'ar harkokin wajen kungiyar tarayyar Turai Federica Mogherini ta ce kungiyar EU da NATO suna aiki wajen karfafa tsaro da kariya daga masu satar yin kutse ta harkokin sadarwar Internet.

Mogherini ta yi wannan kalamin ne yau a Brussels a rana ta biyu na taron ministocin tsaro na kungiyar NATO. 

"A bangaren Tayyar Turai muna karfafa aiki kan satar kutse ta Internet a matakai daban daban. Muna kuma duba yadda za mu karfafa manufofin kasashen kungiyar Tarayyar Turai akan wannan. Haka bangaren NATO ana mayar da hankali sosai domin dakile dukkan wata kafa ta satar kutse ta Internet."

Tun da farko Britaniya da Australia sun zargi bangaren leken asirin Rasha GRU da hannu wajen yin kutse a kafofin sadarwar Internet a kasashe da dama na duniya. 

A waje guda kuma kasar Netherland ta sanar da sallamar wasu jami'an leken asiri su hudu na kasar Rasha bisa yunkurin yi mata kutse ta Internet.

Sakatare Janar na kungiyar ta NATO Jens Stoltenberg ya gargadi Rasha ta dakatar da halayyar da ya kira kasada da ganganci na yin kuste a harkokin Internet na kasashen duniya da kuma rashin martaba dokokin kasa da kasa.