Rasha ta karbi shugabancin kwamittin sulhu na MDD | Labarai | DW | 01.04.2023
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha ta karbi shugabancin kwamittin sulhu na MDD

Rasha ta karbi shugabancin karba-karba na kwamittin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya. Fadar Kremlin ta ce ta shirya sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na shugabancin.

Kasar Amirka ta bukaci Rashar ta gudanar da shugabancin bisa kwarewa yayin da ta yi ikrarin cewa babu wata hanya da za a iya bi wajen hana Rasha jan ragamar kwamittin, duk da kokarin da Ukraine ta yi na ganin hakan bai yiwu ba. Ministan harkokin wajen Ukraine, Dmytro Kuleba ya bayyana shugabancin Rasha a kwamittin a matsayin babban abun kunya ga duniya kana ya bukaci kasashen mambobin kwamittin da su takawa Rashar birki idan ta yi yunkurin wuce gona da iri. Rasha dai za ta ja ragamar kwamittin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a watan Aprilun nan da muke ciki kafin ta mika shugabancin ga kasar Switzerland.