1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha za ta fara amfani da wata sabuwar doka

Zulaiha Abubakar MNA
June 4, 2018

'Yan majalisar dokokin kasar Rasha sun sahalewar shugaba Vladimir Putin damar mayar da martani ga manyan kasashen duniya kan takunkumai.

https://p.dw.com/p/2yupu
Russland Putin bei TV-Rede
Hoto: Getty Images/AFP/M. Klimentyev

Dokar wacce 'yan majalisar dokokin kasar suka kirkira tun bayan da kasar Amirka ta sanyawa Rasha takunkumi cikin watan Afrilun wannan shekara, a halin yanzu ta sahalewa shugaban kasar damar dakatar da alaka tare kuma da haramta cinikayya da dukkan kasashen da suka samu tsamin dangantaka da Rasha a kowanne lokaci.

Dangantaka ta kara tsami tsakanin Rasha da Amirka sakamakon musayar yawu kan rikicin kasar Siriya da kuma batun mutuwar wani tsohon jami'in hukumar leken asirin Rasha a kasar Birtaniya.