Rasha ta ayyana zaman makoki na yini daya | Labarai | DW | 26.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha ta ayyana zaman makoki na yini daya

A wannan Litinin ce aka ayyana hakan a duk fadin kasar domin nuna alhini ga mutanen kasar su 92 da suka rasu a hadarin jirgin sama da ya wakana a tekun Asuwad a daren Asabar washe garin Lahadi


Hadarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan Kirsimeti. 

Shugaban kasar ta Rasha Vladmir Poutine ya bada umarnin a gudanar da kwarararan bincike domin sanin musabbabin faduwar jirgin. Tuni ma dai ya kafa wani kwamiti na musamman a karkashin jagorancin ministan ma'aikatar sufuri na kasar Maxime Sokolov domin gudanar da aikin binciken. 

Daga nashi bangare ministan tsaron kasar ta Rasha ya ce ana ci gaba da gudanar da aikin binciken a gabar ruwan na Bahar Asuwad domin tsamo gawarwakin mutanen da hadarin ya rutsa da su da suka hada da sojojin rundunar mawakan sojan kasar ta Rasha kimanin 60 da 'yan jarida guda tara da kuma ma'aikatan jirgin sun takwas.