Rasha: Navalny ya bayyana gaban kotu | Labarai | DW | 02.02.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha: Navalny ya bayyana gaban kotu

Jagoran 'yan adawar Rasha Alexei Navalny ya yi fatali da zargin saba matakin kotu a kansa, bayan ya gurfana a karon farko gaban wata kotu ta birnin Moscow bisa tuhumarsa da taka doka.

A yayin da aka gabatar da shi a gaban wata kotu, Lauyoyin Alexei Navalny sun yi ta ja in ja da masu gabatar da kara, kan yiwuwar saba matakin daurin talalar da kotu ta yanke masa na fiye da shekaru uku a 2014, laifin da masu zargin ke ganin akwai bukatar tabbatar da daurin adadin shekarun kan Alexeï Navalny a gidan yari.

Rahotanni sun ce an kama daruruwan magoya bayan Alexei Navalny da suka yi dandazo a gaban kotun, makwanni biyu kenan bayan kama wasu tarin jama'a da suka fito zanga-zangar nuna goyon bayansu ga dan adawar.

A ranar 17 ga watan Janairu ne jami'an tsaro suka cafke Navalny bayan ya koma a gida, watanni da kammala jiyar shayar da shi wata guda a wani asibiti da ke nan Jamus.