Rasha: Likitoci sun zargi guba a jikin jagoran adawa | Labarai | DW | 29.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha: Likitoci sun zargi guba a jikin jagoran adawa

Rahotannai daga Moscow babban birnin kasar Rasha sun bayyana yadda jogaran adawar kasar Alexei Navalny ya fito daga asibiti inda likitansa ya nuna fargabar samun guba a cikin gwaje-gwajen da ya gudanar.


A Lahadi da ta gabata aka kai jagoran adawa zuwa asibiti cikin gaggawa daga gidan yarin da yake zaman kaso, yayin da mahukunta suka tsuke baki game da gamsasshen bayanin abinda ya haifar da cutar, jami'an tsaro sun cafke Navalny ne gabanin wata zanga-zanga data gudana a ranar Asabar din data gabata bayan 'yan sanda sun kame kusan mutane da dama daga cikin masu zanga-zangar.

A shekara ta 2011 fadar mulki ta Kremlin ta zargi jagoran adawar Alexei Navalny da laifin tada rikicin siyasa bayan ya jogoranci zanga-zangar kin jinin shugaban kasar Vlamir Putin.