Rasha: Ganawar Putin da Xi Jinping | Labarai | DW | 20.03.2023
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha: Ganawar Putin da Xi Jinping

Ganawar Shugaba Xi Jinping da takwaransa Vladimir Putin ta dauki hankulan kasashen da suka mayar da Rasha saniyar ware saboda mamayar Ukraine.

Shugaba Xi Jinping a Mosko

Shugaba Xi Jinping a Mosko

Shugaban kasar Chaina Xi Jinping ya isa birnin Mosko a ziyararsa ta farko tun bayan da Rasha ta soma mamayar makwabciyarta Ukraine, a jawabinsa ga manema labarai a gabanin ziyarar, Shugaba Xi ya ce,  yana da kwarin gwiwa cewa, ziyarar za ta kasance mai amfani da kara bude wata sabuwar kafa ga ci gaba na zaman lafiya tare da inganta dangantakar da ke tsakanin kasarsa da Rasha.

Ganawar na zuwa ne kwanaki kalilan bayan da Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ICC, ta bayar da sammacin kama shugaban kasar ta Rasha Vladimir Putin, domin tuhumarsa a kan aikata laifukan yaki a kasar Ukraine, a martaninta, Rashan ta ce, ta shirya kalubalantar matakin kotun ICC a gaban shari'a kan sammacin kama Shugaba Putin.