1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Gwamnati na son Alexei Navalny ya koma Rasha

December 29, 2020

Hukumar kula da gidajen yari ta kasar Rasha ta ba fitaccen mai adawa da gwamnatin Kremlin Alexei Navalny wa'adin ya bayyana a gabanta.

https://p.dw.com/p/3nKHj
Russland I Nawalny
Hoto: Shamil Zhumatov/REUTERS

Hukumar ta ce idan har wannan Talata ta wuce ba tare da dan adawar ya gurfanar da kansa a ofishinta ba, to ya kwana da sanin cewa zaman gidan kaso na jiran shi a duk lokacin da ya koma Rasha.


Navalny dai ya kwashe watanni a nan Jamus inda ya ke murmurewa daga gubar da yake zargin gwamantin Rasha ta shayar da shi. Sai dai kuma Rashan ta musanta hakan. 


Sai dai ita hukumar gidan yari ta Rasha ta ce kiran da take masa na da nasaba da wani hukunci da aka yanke wa Navalny a shekara ta 2014, wanda ya yi tanadin jami'ai su rinka sanya ido a kansa. Ta ce ta samu labarin dan adawar ya warke ''sa-rai'', amma yana kauce wa shari'a. To sai dai Navalny ya ce hakan ya nuna cewa hukumomin Rasha sun yarda sune suka shayar da shi guba.