1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An cika shekaru 70 da haramta bauta a duniya

Usman Shehu Usman RGB
December 2, 2021

Shekaru 70 da haramta bauta a duniya amma matsalar na ci gaba da kamari musanman a kasashe masu tasowa da jama'a da dama ke fama da talauci.

https://p.dw.com/p/43kv6
Moderne Sklaverei
Hoto: Bharat Patel

Duk da haramta bauta a duniya da aka yi, amma kuma a wasu kasashen Afirka akwai tsarin bauta da yanzu haka ke faruwa, hukumomin sun kasa magance matsalar. A yanzu haka akwai barazanar cewa matalauta za su kara fuskantar matsalolin da a dole sai sun dogara da wasu wajen tafiyar da rayuwarsu.

Misali a yankin Kayes da ke kasar Mali, har yanzu anan da tsarin bauta. Inda Cheick na Diarra wanda ke zama a kauyen Baramabougou da ke yankin na  Kayes a kasar ta Mali, ya ce, shi kansa ya fuskanci wannan barazana daga  bauta  da ake fadi, inda wata rana ma da kyar ya tsira da rayuwarsa bayan da wasu masu ikirarin cewa su iyayensa ne suka nemi hallaka shi.

Karin Bayani: A Nijar har yanzu ana bautar da mutane

Junge Lastenträger Ghana
Matsalar bautar da yara na karuwaHoto: picture-alliance/dpa

Diarra ya ce,  a shekarar 2018 ko noman gonakinsu ba su iya yi ba, domin wadanda ke cewa su ne iyayen gijinsu sun hanasu, suka fada masu cewa su je su yi masu kasuwanci a shaguna, ko su yi masu noma ko kuma su bar kauyen baki daya. Ita kuwa Kungiyar Temedt ta tsayane don haramta bauta da ake yi a kasar ta Mali. Raichatou Walet Altanata ita ke shugabantar kungiyar. A cewarta wasu lokutan hukumomi kan dauki irin wannan lamarin a matsayin rikici tsakanin mutane, ko kuma wani laifi amma kuma ba a duba lamarin a matsayin bauta.  

Karin Bayani: Ranar yaki da bautar da yara ta duniya

Pakistan Arbeiter Schulden Sklaverei Arbeitsbedingungen
Ana ci da gumin marasa karfi a Pakistan Hoto: Getty Images/AFP/A. Hassan

Tun a shakara ta 1949 aka aiyanan bauta a mastayin laifi a fadin duniya, inda Majalisar Dinkin Duniya ta saka ranar biyu ga watan Disamba a matsayin ranar yaki da bauta, amma yanzu shekaru 70 bayan haramtawar har yanzu ana samu wadannan matsaloli. An dai yi kiyasin akalla mutane miliyan 24 ke aikin fin karfi a fadin duniya, kama daga aiyukan cikin gida da harkar noma.

A Nahiyar Afirka kasashen Jamhuriyar Nijar da Sudan da Mali da Mauritaniya da kuma Chadi sune ke ci gaba da aiki da bautar da mutane kamar yadda kungiyar yaki da bauta ta duniya ta sanar.  A cewar masana, annobar corona da ta bulla a 'yan shekarun nan da yi sanadin talauta mutane da yawa, abin da kuma ya kassara talakawa shiga yawon duniya, inda ‘yan ci rani ke shiga ko wane aiki suka samu ciki har da aiyuka masu hatsarin gaske, inda hakan ke sa ana ci da guminsu.