1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bautar da kananan yara a kasar Mali

December 7, 2011

Hukumar kare hakkokin bani adama ta kasa da kasa Human Right Watch da bayyana rahoton gallazawa kananan yara a wuraren tonan zinare a kasar Mali.

https://p.dw.com/p/13O9M
Hoto: DW

Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa wato Human Rights Watch ta wallafa wani rahoto dake nuna cewa bautar yara kanana ta zama ruwan dare gama duniya, musammam ma wuraren da ake tonar zinare a kasashen Afrika.

Rahoton ya duba yadda ake bautar da yara a wuraren tonon zinare na kasar Mali.

Kasar Mali, ita ce kasa ta uku a cikin kasashen da suke yankin Afrika masu arzikin zinare wadanda suka hada da Burkina Faso, Cote d Ivoire, Ghana, Guinea, Niger, Nigeria da Senegal.

Duk da yake kasar tana da dokoki masu tsauri dangane da bautar yara kanana da bada ilmi kyauta, gwamnatin kasar ta yi wa dokokin rikon sakainar kashi da nuna halin ko oho.

Binciken wanda kungiyar kare hakkin bil adam ta duniya ta gabatar, ya yi tonon silili game da munanan hadurran da ake sa yara kanana a ciki wajen hakar zinare kamar yanda jami'ar kungiyar Julian Kippernberg ta bayyana:Abun da binciken da muka yi ya nuna mana game da aikin hakan zinare a kasar Mali shine, yara fiye da dubu ishirin ne suke aiki a rijiyoyin hakan zinare da suke fitowa daga kasar a cikin munanan yanayi masu hadari. Misali, suna daukan kayan da suka fi karfin su, suna kuma shakar sinadarai masu guba.

Babbar Jami'ar kula da yancin yara ta kungiyar, Julian Kippernberg ta bayyana cewa binciken da suka gudanar ya nuna cewa wasu daga cikin yaran suna aikin tare da iyayen sune, wasu kuma da kansu suke tattaki har rijiyoyin hakar zinaren inda suke fuskantar zalunci daga dangi, ko ma wadansu daban ta hanyar kwace musu dan kudin da suke samu. Wasu yara matan ma sukan fuskanci fyade da shiga karuwanci. Jami'ar ta kara da bayyana dalilan da ya ke sa yara suna shiga irin wannan mummunar hali:

Babban dalilin shine talauci. Mafi yawancin yaran da su ke aiki a rijiyoyin hakan zinaren iyayen su na aiki a wurin. Kudin da suke samu ba wani abin a zo a gani bane. Ga haraji da suke biya ga hukumomin, sannan kuma yan kasuwan da suke siye a hannun su ba su basu wani abin kirki.

Gwamnatin kasar bata maida hankali wajen karfafa dokokin da suke hana bautar kanana yara a rijiyoyon hakan zinare ba, Sannan bata maida hankali wajen wajabata ilmi da tabbatar da bada shi kyauta a wuraren da rijiyoyin hakan zinare suke ba. Misali, har yanzu iyaye da dama suna biyan kudin makaranta, makarantun suna da nisa kuma babu kayan koyar wa danan koyon karatu a cikin su.

Gwanmatin kasar Mali ta bullo da wani shiri na kawar da bautar yara kanana a watan Yuni na bana, amma har yanzu babu shi a zahiri.

Kuma babu wani dubiya da ake yi na rijiyoyin hakar zinare domin tabbatar da tsirar kananan yara daga aiki a cikinsu, bayan kuma doka kasar Mali da ma ta duniya baki daya ta haramta aiki a tsauraran yanayi masu hadari a rijiyoyin hakar ma'adinai, da aiki da sinadari mai guba na mercury ga duk wanda bai kai shekaru goma sha takwas ba.

Julian Kippernberg, ta ce ba haka banza bane Gwamnatin Mali tasa ido tana kallo ana tabka wannan ta'asan:

Daya daga cikin dalilan da yasa haka shine hukumomin da suke da karfi a yankunan suna amfana ne daga irin wadannna rijiyoyin hakan zinaren. Shi yasa abin bai dame su ba, kuma basu da niyyar magance matsalolin bautar yara kanana, amfani da sinadari mai guba da dai sauran wadansu al'mura da suka shafi yancin bil adama.

A duk shekara, ana samun zinare har na dala miliyan 218 daga irin wadannan rijiyoyin hakan zinaren da ake bautar da kananan yara a ciki daga kasar Mali.

Mawallafiya: Hawwah Abdullahi Gambo

Edita: Yahouza Sadissou Madobi