1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Hawa keke na kara samun tagomashi a duniya

June 4, 2019

Hawan keke na cikin nau'oin motsa jiki kuma Majalisar Dinkin Duniya ta ware uku ga watan Yuni a matsayin ranar bunkasa dabi'ar hawa keke.

https://p.dw.com/p/3JoSj
Still aus DW Eco Africa - E-Bikes
Hoto: DW

A jihar Kaduna da ke Najeriya wannan rana ta zo a daidai lokacin da jama'a ke ci gaba da rungumar hawa kekuna a kashin-kansu ba tare da wani kamfe daga gwamnati ko kungiyoyi ba. Mukhtar Musa wani magidanci ne da ya kwashe fiye da shekaru goma sha biyar yana hawa keke, duk da cewa a yanzu za a iya cewa kekunan da sun bace amma Mukhtar bai daina hawa keke ba inda ya koma hawan na zamani.

Ba magidanta kadai ke hawa keke ba, a ‘yan shekarun nan ana ci gaba da samun karuwar matasa da kan hau keke domin kwalisa. To sai dai ga matashi Umar mai shekaru 20 da haihuwa. Matashi Umar dai na fatan daina hawa keke da zarar ya samu kudin sayen mashin to amma ga Mustapha Zubairu keke ya kasance masa tamkar hanta da jinni. Domin a kowace rana ya kan yi kamar mintuna 80 yana taka fedar keke.

A shekarar da ta gabata Majalisar Dinkin Duniya ta ware rana ta musamman (uku ga watan Yuni no kowace shekara) domin bikin ranar masu hawa keke ta duniya domin tulawar abubuwan da suke shafar hawan keke a sassa dabam-dabam na duniya.

Yayin da ake bikin ranar masu hawa keke ta duniya a wannan wata na Yuni fatan masu kare muhalli shi ne jama'a su fifita hawa kekuna a maimakon motoci da babura wadanda a ilmance ke barazana ga mutum da duniyarsa.