Rahoton IAEA kan shirin nukiliyar Iran | Labarai | DW | 16.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rahoton IAEA kan shirin nukiliyar Iran

Hukumar da ke sanya idanu kan makamshin nukilya ta Majalisar Dinkin Duniya IAEA ta ce Iran ta kammala shirye-shirye na cigaba da shirinta na nukilya.

Titel: Iran Atom Natanz . Unterirdische Anlage für Uran-Anreicherung in Natanz in Zentral-Iran . Besuch des Präsidenten Mahmoud Ahmadinedjad Quelle: Fars

Bildergalerie Iran Atomkraft Atom

A wani rahoto da fitar a wannan Juma'ar hukumar ta IAEA ta ce an gina wajen ne karkashin wani tsauni kuma aiyyukan da wajen zai iya yi, zai rubanya kokarin na Iran na cigaba da yunkurin da ta ke yi na mallakar makaman kare dangi.

Tuni dai mahukuntan Iran din su ka ce wannan batu ba shi da tushe bare makama kuma sun sake jaddada mastayinsu na cewar shirin nukilar na su fa na zaman lafiya ne, hasali ma bai wuce na samar da makamshi ba, to sai dai duk da wannan kalamai na mahukuntan na Iran, Amurka da Isra'ila na cigaba da nuna shakku game da shirin.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Muhammad Nasir Awal