Rahotanni daga Nijeriya sun ce Umar ´Yar Aduwa ya fara samun sauki | Labarai | DW | 07.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rahotanni daga Nijeriya sun ce Umar ´Yar Aduwa ya fara samun sauki

Dan takarar shugabancin Nigeria karkashin inuwar jam´iyar dake jan ragamar mulki Umaru Musa ´Yar Aduwa ya fara samun lafiya a wani asibiti da aka kwantar da shi dake nan Jamus, inji kakakin sa Ndu Ughamadu. Mista Ughamadu ya karyata rahotannin da kafofin yada labaru suka bayar da farko cewa ya suma kuma bai farfado ba. Wata sanarwa da jam´iyar PDP ta bayar na nuni da cewa a jiya talata Umaru ´Yar Aduwa ya bar Nijeriya zuwa Jamus don duba lafiyarsa kamar yadda aka saba, kuma zai koma gida cikin lokaci don ya ci-gaba da yakin neman zabe. ´Yar Aduwa mai shekaru 56 ya na fama da ciwon koda kuma jita-jita game da lafiyar sa ta dabaibaye yakin neman zabensa. A ranar daya ga wannan wata na maris ya fadawa kamfanin dillancin labarun Reuters cewa ya gamsu da lafiyar sa.