Rahota kan karuwar hatsura a tituna | Siyasa | DW | 20.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rahota kan karuwar hatsura a tituna

Hukumar Lafiya ta Duniya wato WHO ta ce kimanin mutane miliyan daya da dubu 250 ne ke rasa rayukansu duk shekara sakamakon hatsura

A rahoto da ta fidda hukumar ta ce galibin asaran rayuka da ake samu sakamakon hatsuran na faruwa ne a kasashen masu tasawo ciki kuwa har da Amirka da Najeriya.

A cikin rahoton da ta fidda mai shafi 340, WHO din ta ce abubuwa da dama ciki kuwa har da rashin bin ka'idar tuki da tsufan da ababen hawa suka yi musamman ma a kasashen da ke nahiyar Afirka, da kuma gudun fiye da kima ne, sune ke haifar da hatsura a kan titunan wadannan kasashe.

A zantawarsa da DW Dr. Etienne Krug da ke kula da sashen da ke sanya ido kan cutuka da nakasa da kuma kiyaye hatsura, ya ce baya ga direbobin da hatsura ke shafa, mutane da ke tafiyar kafa da masu kekuna da babura, sua daga cikin wanda wannan matsala ke rutsawa da rayuwarsu."Afirka na daga cikin wuraren da wannan matsala ta fi kamari, a Afirka ne har wa yau aka fi samun yawan mutuwar mutanen da ke tafiya a gefen tituna. Duk da cewar akwai ci-gaba a wasu bangarori, amma fa hakan bai taimaka wajen kawar da matsalar ba, musamman ma dai ta kiyaye lafiyar mutane".

Tarayyar Najeriya dai na daga cikin kasashen da rahoton na WHO ya ambata, a matsayin wanda matsalar samun hatsura kan tituna ta fi kamari. Wannan ne ma ya sanya na tambayi Dr. Krug dalilin da ya sanya ake samun wannan matsala, duk kuwa da yunkurin da hukumomi suka ce suna yi na kiyaye hatsari, musamman a rubu'in karshe na kowacce shekara.

"Ya ce ba ko wane fasinja ne ke mutunta dokar sanya belt na kariya a cikin mota a Najeriya. Ko kuma kauracewa yin tuki bayan kwankwadar barasa. Baya ga wannan kuma akwai batu na ingancin motoci, domin kuwa akwai su da dama a kan tituna, yayin da sabbin basu da abubuwan da ke taimakwa wajen kariya idan hadari ya auku."

Yayin da rahoton na WHO ke nuni da irin yawaitar hatsuran da ake samu Najeriya sanadiyyar matsalolin da Dr. Krug ya shaidar, Aliyu Wada Rurum jami'i a hukumar KAROTA da ke kula da kai-komo na ababen hawa a jihar Kano, wadda ke kan gaba wajen yawan al'umma a Najeriya. Ye ce matakan da suke dauka a baya-bayanan sun taimaka wajen rage matsalar, kuma nan gaba ne ma za a fi ganin tasirinsu.

Rahoton na WHO ya bukaci da a maida hankali wajen tilasta wa mutane su yi abinda ya kamata, yayin da suke kan tituna musamman ma abin da ya danganci sanya hular kwano, bin ka'idar titi da sanya jami'an tsaro da za su tabbatar direbobi sun gujewa yin gudun da ya wuce kima.

Sauti da bidiyo akan labarin