Rage albashin masu rike da mukaman siyasa a Najeriya | Siyasa | DW | 26.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rage albashin masu rike da mukaman siyasa a Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bada umarnin zaftare albashin 'yan siyasa da ke lamushe milliyoyin Nairori na kasar.

A wani abun da ke zaman kama hanyar kai karshen kace-nacen da ta mamaye albashin masu rike da mukamai na siyasa a cikin tarrayar Najeriya, shugaban kasar Muhammad Buhari ya bada umarnin zaftare albashin da ma alawus-alawus din da kan lamushe milliyoyin Nairori na kasar.

Tuni dai shugaban ya baiyyana zaftare kaso 50 cikin 100 na albashin nasa a wani abun da ke zaman alamar sadaukarwa ga kasar da ke cikin halin ni'yasu ga batun kudi a halin yanzu.

Kokarin maimaita hakan dai ya ce tura da turjiya a cikin majalisun kasar biyu da suka ja daga ga kokari na yanke kaso 30 cikin 100 na daunin nasu domin mutunta yanayin da kasar ta Najeriya take ciki a halin yanzu.

Nationalversammlung in Abuja, Nigeria

Ginin majalisar wakilan Najeriya a Abuja

Buharin da ya gana da jami'an hukumar tsara albashi da alawus-alawus na masu rike da mukamin na siyasa dai ya ce rashi na hankali ne ga hukumar na ware makudai na kudi da nufin biyan bukatar manya a yayin da ragowar 'ya'ya na kasa ke cikin tsaka mai wuya.

Tuni dai hukumar a fadar shugabanta Elias Mbam ta fara aiki na ragin da a cewarsa take shirin kammalawa a cikin watan Satumban da ke tafe.

"A yanzu haka muna sake nazarin daunin masu rike da mukaman na siyasa, kuma zai yi la'akari da halin da kasa take ciki a yanzu. Kuma ya kunshi matakai. Ba magana ce ta eh ko a'a ba. Magana ce ta tsari na matakai, kuma za mu yi la'akari da yanayi na zamantakewar yanzu."

Kafin yanzun dai ana zargin masu rike da mukaman na siyasa da kwashe dubban miliyoyin Nairori da sunan albashi da alawus din. Can a majalisun tarrayar kasar biyu dai akalla Naira milliyan dubu 150 ne ke tafiya a shekara wajen haskaka rayuwar mutane 469 da kuma mukarraban da ke musu aiki domin doka.

Nigeria - Präsident Muhammadu Buhari

Buhari ya kuduri aniyar rage kashe kudi don biyan bukatun manya

Ana dai kallon sabbabi na matakan a matsayin kokari na nuna shugabanci a bangaren mahukuntan da suka dauki lokaci suna ta korafin rashin kudin yin aikin jama'a duk da alkawuran sauyin da suka zagaye tudu da rafukan kasar ta Najeriya yayin zabe.

To sai dai kuma a tunanin Hon Jagaba Adams Jagaba duk wani ragin da zai isa aljihun majalisar to yana da tasiri a ragowar al'umma ta kasa.

"Duk da cewar dai a yawa na kudi ragin da ake tunanin zai iya kamawa daga kaso 30 ya zuwa 50 cikin 100 bashi da tasirin a fito a fada."

A siyasance dai na zaman alama ta damuwa ta shugabanni na siyasar da ma sauke kansu zuwa matsayin talakawa a fadar Dr Umar Ardo da ke zaman masani na siyasar kasar ta Najeriya.

'Yan majalisar kasar ta Najeriya dai sun darma sa'a a tsakanin 'yan uwansu na akalla kasashe 29 da wata mujallar birnin London ta yi sharhi kansu.

An dai kiyasta kowane dan majalisa ta wakilai na samun abun da ya kai Naira miliyan 30 da sunan albashi da alawus a shekara adadin kuma da ya ninka samu na kasar da misalin kaso sama da 100 cikin 100.

Sauti da bidiyo akan labarin